Posts

Showing posts from December, 2023

kisanda Dan chena yayiwa ummita akano yanzu yazama tarishi Allah yakaregaba Yakima kare sauran mutane daga shiga iftila,I narayuwa mararkyau

Image
Dan China Da Ya Kashe Ummita Ya Bayyana Irin Makudan Kudin Da Ya Kashe Mata Yanzunan Majiyar Ta Sami Wallafa Daga Shafin Garkuwanarewa Dake Nuni Da Cewar Dan China Da Kashe Ummita Ya Bayyana Irin Makudan Kudin Da Ya Kashe Mata Kamar Yadda Suka Wallafar Cewar Dan China da ake zargi da kisan Ummita ya ce Naira Miliyan 60 ya kashe mata A yau Laraba ne dai dan Chinan nan mai suna, Frank Geng Quangrong, wanda ake zargi da kisan masoyiyar sa Ummukulsum Sani, wacce akafi sani da Ummita, ya fara kare kansa a kotu. Quangrong ya shaida wa kotun cewa shi Musulmi ne kuma ya na aiki a wani kamfanin tufafi a kasuwar Kantin Kwari ta jihar Kano. Ya bayyana cewa sun hadu da marigayi Ummita ne a 2020, bayan da ta samu lambar wayar sa a wajen wata kawar ta, inda ta nuna tana son shi kuma za ta aure shi. Jaridar Justice Watch ta rawaito cewa dan Chinan ya ce bayan ya amince da ita, sai su ka fara soyayya, inda ta rika karbar kudade a wajen sa, ya kara da cewa “haka na rika bata duk abinda ta roke ni sabo ...